#Sabuwar Shekara1441.
Mun shiga Sabuwar Shekarar musulunci, Shekarar da ta wuce zataimana Shaida wanda yasamu kyakkyawar Shaida wanna shine ya rabauta. Wanda kuma yasamu akasin haka to yayi kokarin gyara kuskurensa. Hakika bulowar Rana da da wata da caccanzawar yanayi ayoyine ga ma'abota hankali Tafiyar kwanaki Alamace datake nuna muna cin wani yanki na rayuwar mu, tafiya mukeyi lokaci bai dawowa, nesantar Daniya Muke kusantar lahira muke. Muyiwa kanmu bincike inda mukai Aikata kyakkyawan aiki sai mucigaba inda mukai kuskure mu gyara muduba muga mai mukatanadar a nan gaba . Mutuba daga zunuban mu mubar cewa sai nan gaba domin rayuwar mu ba a hanunn mu take ba. Muduba Abinda yai saura na rayuwar mu domin muyi aiki nagari, mu gaggauta aikata Alkairi. mu Shiga Sabuwar Shekara da kyakkyawan fatan Samun nasara Da cigaba a dukkan Al'amuran mu na da kyautatawa Allah zato Zai kawo mana Sauqi Arayuwar mu Insha Allah. *1 Al-Muharram 1441* *1 September 2019* #IshaqShuaibuIbrahim