ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)

Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu

 
⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪

 ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)

DARASI NA 1

 عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ، قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " مَنْ يُرِدِ اللَّهُ بِهِ خَيْرًا يُصِبْ مِنْهُ ". 

 FASSARA

An karɓo daga Abu Hurairah (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Wanda Allah ya nufe shi da alkhairi, sai ya jarabce shi." SAHABIN DA YA RAWAITO Sunansa: Abdurrahman Ibn Sakhr Alkunyarsa: Abu Hurairah Nasabarsa: Addausiy Alyamāniy Almadaniy Rasuwarsa: shekara ta 57 B.H Darajarsa: yana cikin ajin farko (الطبقة الأول)

Hadisansa: Ya rawaito hadisai guda 5374 (ya fi dukkanin Sahabbai rawaito hadisi daga Manzon Allah) DARASI DAGA HADISIN Annabi (S.A.W) yana yiwa muminai masu kamalar imani cewa: a cikin duk wata jarabawa da za su iya gani a wannan duniyar, akwai wani alkhairi da Allah (S.W.T) yake nufinsu da shi. Don haka su yi haƙuri, su daure kuma su koma zuwa ga Allah (S.W.T). 

Za mu ci gaba bayan awanni 24 in sha Allah. 

© Adam Sharada

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Nana Khadija (R.A)

177 Sunan Tirmizi

Riyadus Salihin