MAKAMASHIN "WIND ENERGY": IKON ALLAH A CIKIN KIMIYYAR PHYSICS


 MAKAMASHIN "WIND ENERGY": IKON ALLAH A CIKIN KIMIYYAR PHYSICS


00|| SHIMFIƊA

Kimiyyar Physics tana jujjuyawa ne akan "matter", wato komai (mai rai da mara rai) da ake iya taɓawa ko a ji yanayinsa a jiki ko ma a iya hasashensa a zuci. Ita "matter" a tushenta nau'i 3 ce; solid (daskararre), liquid (mai ruwa-ruwa) da kuma gas (iska). Yanayin siffofi da tasirin ƙarfe wajen gudanar matter shi ne fannin da malaman Physics ke kira "Behavior of Matter".


Daga nan kimiyyar Physics ta yi ta reshe cikin fannonin kimiyya, ta shiga Labarin Ƙasa (Geography) ta haifi Geophysics, ta shiga  kimiyyar halittu masu rai (Biology) ta haifa musu Biophysics, ba ta tsaya nan ba ta faɗa cikin hatta halayyar ɗan adam (Psychology) ta ajiye musu ɗanta mai suna Psychophysics, sannan ta luluƙa ta bar wannan duniyar tamu (Earth) ta faɗa Sama-jannati (Astronomy) ta haifi Astrophysics. Dama su Chemistry (Chem-is-try) kada su ji labari, wannan kam wata tsoka ce ƴar ƙarama da aka reɗo ta daga jikin ragon layyar kimiyyar Physics 😍


NB: Idan ƴan Chemistry suka yunƙuro ku ce musu Sir Earnest Rutherford (1871-1937) ne ya ba mu ratayar zomon a faɗinsa: “all science is either physics or stamp collecting.” 


01|| MENENE WIND ENERGY?

Wind Energy ko "wind power" shi ne makamashin iska da ake sarrafawa a samar da wutar lantarki da muka sani. 


Malaman Physics sun samar da nazariyyar yadda za a iya zuƙar iskar nan da muke shaƙa a killace ta, sannan a sarrafa ta bisa hikima da dabara ta ɗan adam har ta iya sauyawa daga iska zuwa wutar lantarki, da za a iya cin moriyarta a zamantakewa. A wannan gaɓar ne suka samar da wata na'ura mai zuƙo iska tare da killace ta a bankin iska mai suna "Wind Turbine".


Shi wannan wind turbine ɗin bayan ya farauto iska daga sararin Allah, sai ya shigar da ita cikin bankin iskar da ke jikinsa, a cikin bankin kuma akwai na'urar "generator" da za ta sauya fasalin sinadarin wind energy zuwa sinadarin lantarki abin da ake kira: transformation of energy from kinetic to mechanical. Daga nan sai hasken lantarki ya samu.


Yau a kimiyyance kusan ba abin da yake cin kasuwa irin binciken "Energy and Environment", domin katange duniya daga barazanar ƙarewar man fetur da rashin wadatacciyar lantarki da ake fama da ita.


02|| DAGA INA AKA SAMU MAKAMASHIN WIND ENERGY?

Daga cikin mafiya girman fannonin Physics da suka sauya akalar duniya akwai "Renewable Energy" wanda yake nazarin yadda za a iya samar da wani makamashin da zai amfani duniya musamman ta fuskar lantarki. Wannan nazariyya ta mayar da hankali musamman akan wasu makamashai guda 3 kamar haka:


I- Solar: wato hasken rana (Solar Energy)

II- Wind: Ita ce iskar nan da muke shaƙa (Wind Turbine)

III- Water: shi ne ruwa musamman na manyan dama-damai da rafuka masu gudana (Water Turbine)


Duka waɗannan suna tsirowa daga ikon ALLAH (S.W.T) da buwayarSa da nufinSa, saboda gamammen jin ƙanSa ga halittunSa masu rai da marasa rai. Saboda rashin TAUHIDI malaman Physics da sauran malaman kimiyya suna cewa, wai waɗannan abubuwa sun samu ne naturally, wato kawai sun kasance ne a cikin kaunu ba tare da wani taƙamaimai din tushe ba. Sun dai yarda an samar da su, amma ba su san ALLAH (S.W.T) ne ya samar ba, galibinsu ma ba su yarda da samuwarSa ba kacokan.


03|| ALƘUR'ANI DA WIND ENERGY

Mu musulmi da muka rabauta da shiriyar Alƙur'ani maigirma Alƙur'ani ya sha nanata mana cewa Allah (S.W.T) shi ne ya halicci kowa da komai:


اللَّهُ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ

(Az-Zumar: 62)


A iya nan kaɗai mun wadatu. Kuma ita ce gaɓar da muke tambayar masu inkarin samuwar Allah (S.W.T); indai ba Allah (S.W.T) ne da mu musulmi mike bautawa ya halicci komai ba, to waye? 


Game da wind energy mu leƙa Alƙur'ani maigirma:


وَهُوَ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْرًا بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا أَقَلَّتْ سَحَابًا ثِقَالًا سُقْنَاهُ لِبَلَدٍ مَّيِّتٍ فَأَنزَلْنَا بِهِ الْمَاءَ فَأَخْرَجْنَا بِهِ مِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ ۚ كَذَٰلِكَ نُخْرِجُ الْمَوْتَىٰ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ

Kuma Shi (Allah) ne ya aika ISKA tana mai bushara da yalwar RahamarSa, har ta kai idan ta ɗauki girgije mai nauyi (wanda ke ɗauke da ruwa) sai mu juye shi akan matacciyar ƙasa, sai mu saukar da ruwa da shi, (daga nan) sai kuma mu fitar da dukkan dangogin kayan marmari.....

(A'arāf: 57)


A wannan ayar Allah (S.W.T) ya ce Shi ne yake turo da wind energy ɗin kansa! Da bai turo mana iskar ba, da ɗan adam bai samu ƙwaƙwalwar tunanin yadda zai iya sarrafa iskar ba zuwa wani abu daban.


اللَّهُ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ فَتُثِيرُ سَحَابًا فَيَبْسُطُهُ فِي السَّمَاءِ كَيْفَ يَشَاءُ وَيَجْعَلُهُ كِسَفًا فَتَرَى الْوَدْقَ يَخْرُجُ مِنْ خِلَالِهِ فَإِذَا أَصَابَ بِهِ مَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ إِذَا هُمْ يَسْتَبْشِرُونَ

Allah (S.W.T) Shi ne yake tura iska ta tunkuɗo girgije sai ya baje a sama yadda Allah ya so.....

(Ar-Rūm: 48)


وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ يُرْسِلَ الرِّيَاحَ مُبَشِّرَاتٍ وَلِيُذِيقَكُمْ مِنْ رَحْمَتِهِ وَلِتَجْرِيَ الْفُلْكُ بِأَمْرِهِ وَلِتَبْتَغُوا مِنْ فَضْلِهِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Daga cikin ayoyinSa kuma; shi ne yake tura iska tana mai bushara, sannan don ya ɗanɗana muku zaƙi daga yalwatacciyar RahamarSa.....

(Ar-Rūm: 46)


Wato, Allah (S.W.T) ya aiko iska don ya isar mana da ni'imarSa mai daɗi da zaƙi gare mu mu mutane. A cikin ni'imomin ne ma aka samu wind energy. Kuma samar da wannan ni'imar ta iska, dalili ne mai ƙarfi da yake tabbatar da samuwarSa (S.W.T).


وَٱخْتِلَٰفِ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن رِّزْقٍۢ فَأَحْيَا بِهِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَتَصْرِيفِ ٱلرِّيَٰحِ ءَايَٰتٌ لِّقَوْمٍۢ يَعْقِلُونَ

...... da kuma sarrafa ISKA, (duka) ayoyi ne ga ma'abota hankali.

(Al-Jāthiyah: 5)


Ma'ana: gudanar da iska da sarrafa ta dalili ne mai ƙarfin gaske game da samuwarSa da ɗayantakarSa a wajen bauta, amma ga ma'abota lafiyayyen hankali.


04|| ƊAURAYA

Babban abin da Physics yake nuna mana; shi ne tabbatar da dalilin faruwar wani abu. Idan har mun gamsu da samuwar makamashin wind energy, ba makawa za mu gamsu da danganta samuwarsu ga maƙagin halitta Allah (S.W.T). Domin da a ce bai halicci wind ba, to da tunanin ɗan adam ma ba zai kai wajen ba, ballantana ya samu zarafin tunani akai.


Wannan ma dalili ne ga mulhidai masu inkarin samuwar Allah (S.W.T) ya kamata su ƙulle kansu a ɗaki su nazarce shi da idon basira, zai taimaka wajen ceto zukatansu daga mugun tunanin falsafar metaphysics da ya ruɗe su.


(C) Adam Sharada


#KimiyyaDaAddini #Physics #energy 

#adamsharada

Comments

Popular posts from this blog

Nana Khadija (R.A)

177 Sunan Tirmizi

Riyadus Salihin