Posts

Showing posts with the label ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)

ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)*

Image
Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu Telegram ⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪ *ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)*   *HADISI NA 9* عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " رُبَّ أَشْعَثَ مَدْفُوعٍ بِالْأَبْوَابِ، لَوْ أَقْسَمَ عَلَى اللَّهِ لَأَبَرَّهُ ". FASSARA An karɓo daga Abu Hurairah (R.A). Haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya kasance; gashinsa ya duddunƙule (saboda rashin wanka), jikinsa ya yi kaca-kaca (saboda tsabar talauci), wanda idan ya yi sallama za a tsayar da shi a bakin ƙofa (saboda tsabar talaucinsa): da zai yi rantsuwa ga Allah (kan wani abu), tabbas da sai Allah ya kuɓutar da shi!" Muslim ne ya rawaito DARASI - Allah (S.W.T) ba ruwansa da dukiya ko kuɗi da ɗan adam ya mallaka, Allah ya fi ƙaunar zuciya mai taƙawa da ayyuka na ƙwarai. - Duk wanda ya ke da taƙawa ga Allah (S.W.T) ko da a ce shi ya fi kowa talauci a garinsu, da zai roƙi Allah wani abu, tabbas sai Allah ya amsa masa, saboda ku...

ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)

Image
 Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu Telegram ⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪ ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W) HADISI NA 8 عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " لَا يَسْتُرُ عَبْدٌ عَبْدًا فِي الدُّنْيَا، إِلَّا سَتَرَهُ اللَّهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ". FASSARA An karɓo daga Abu Hurairah (R.A). Daga Annabi (S.A.W) ya ce: "Babu wani bawa da zai suturta wani bawan a duniya, face (shi ma) Allah ya suturta shi ranar alƙiyama." Muslim ne ya rawaito FA'IDA - Alƙur'ani ya ambaci kalmar الدنيا sau 115 - Alƙur'ani ya ambaci يوم القيامة sau 70 DARASI - Yana koya mana taimakon juna da jin ƙai ga mabuƙata. - Yana koya mana rufawa musulmi wanda ya faɗa cikin kuskure asiri, da kamewa daga yaɗa wani mummunan halinsa da ya ɓoyu. - Yiwa mai aikata dangogin saɓo kamar shirka, bidi'a da manyan zunubai nasiha da nusarwa cikin hikima, yana cikin suturce musulmi daga masifa. Za mu ci gaba bayan awanni 24 in sha Allah. Faceboo...

ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)

Image
Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu    Telegram Hadisi Na 06 ⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " لَتُؤَدُّنَّ الْحُقُوقَ إِلَى أَهْلِهَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ، حَتَّى يُقَادَ لِلشَّاةِ الْجَلْحَاءِ مِنَ الشَّاةِ الْقَرْنَاءِ ".  FASSARA An karɓo daga Abu Hurairah (R.A). Haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Lallai za a mayarwa da kowane mai haƙƙi haƙƙinsa ranar alƙiyama! Hatta akuya mai mara ƙaho, za a karɓar mata haƙƙinta daga akuya mai ƙago (idan ta taɓa tunkuyinta)." Muslim ne ya rawaito   DARASI - Yana bamu labarin adalcin Allah (S.W.T), wajen karɓarwa duk mai haƙƙinsa a hannun wanda ya zalunce shi a nan duniya. - Duk wani aiki da muke aikatawa a wannan duniya a rubuce yake, kuma tabbas sai Allah (S.W.T) ya yi mana hisabin ayyukanmu ranar alƙiyama. - Hadisin dalili ne akan tashin dabbobi da duk wata halitta mai rai a ranar alƙiyama. Domin yin hisabi tsakaninsu. - Idan har ...

ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)

Image
Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu Telegram ⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪ *ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)* *HADISI NA 5* عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " مَا أَسْفَلَ مِنَ الْكَعْبَيْنِ مِنَ الْإِزَارِ فَفِي النَّارِ ". FASSARA An karɓo daga Abu Hurairah (R.A), daga Annabi (S.A.W) ya ce: "Abin da ya yi ƙasa da idon sawu (idon ƙafa) na tufafi, yana wuta." DARASI Hadisin yana bayanin inda ya kamata tufafin musulmi namiji ya kasance. Sanya tufafi (riga ko wando) su wuce idon sawu saɓo ne da Allah zai iya ƙona wannan ƙafar da wuta ranar alƙiyama. Hadisin yana tabbatar da cewa; ɗage tufafi ga namiji koyarwar Manzon Allah (S.A.W) ce, don haka duk wanda yake izgilanci ga masu aikata hakan cikin musulmi, to tabbas ya yi izgilanci ga saƙon Manzon Allah (S.A.W) ne. © Adam Sharada 9th Safar, 1443 16th September, 2021

ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)

Image
Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu ⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪ *ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)* *HADISI NA 4* عَنْ أَبُو هُرَيْرَةَ ، عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَنَّ دَاوُدَ عَلَيْهِ السَّلَامُ كَانَ لَا يَأْكُلُ إِلَّا مِنْ عَمَلِ يَدِهِ. FASSARA An karɓo daga Abu Hurairah (R.A) daga Annabi (S.A.W) ya ce: "Haƙiƙa Annabi Dawud (A.S) ya kasance ba ya ci sai (daga) abin da hannunsa ya aikata." ANNABI DAWUD (A.S) - Allah (S.W.T) ya aiko shi da Manzanci kuma ya ba shi littafin Zabura (Suratun Nisa'i: 163). -Allah (S.W.T) ya bawa Annabi Dawud (A.S) fasaha ta iya bayani (Suratu Sād: 20). - Yana cikin Annabawan da Allah (S.W.T) ya aikowa Banu Isra'eela. - Alƙur'ani ya ambaci suna Annabi Dawud sau 16 a cikin surori 9. DARASI - Hadisin yana koya mana ƙoƙarin neman na kai. Kada musulmi ya zama cima-zaune. - Akwai yabo ga Annabawa da siffanta su da jarumta da ƙarfin zuciya. Ta yadda ba sa roƙo ko maula. - Yana kuma koya ma...