H
1. #Annabawa Allah ta'ala yana zabar Annabawa da manzanni daga cikin mutane domin su shiryar da su sukuma yi kira izuwa gabautar Allah. Farkon Annabi shine Annabi Adam na karshe kuma cikamakin Annabawa shine Annabi Muhammad (s.a.w), bayansa babu wani Annabi da zaizo. Dukan su 'yan uwa juna, a i'mani sanan kuma masu kirane zuwa da a bautawa ubangijinsu. Dukk da dokokinsu sun banbanta amma suna yada aqeeda iri daya (itace bautawa Allah shi kadai) Dukan manzanni Allah ya tsare su daga kirkirar wani abu dazuwciyar su take so. Kamar yin hukunci da sarran su, fadawa manyan zunubai, ragi ko qari a addini. Basa aikata haka Allah yakaresu. Allah ya shiryar dasu da aikata nagarta a dukkan al amuransu na rayuwa. Duk dacewa su ma mutanene, zasu iya yin kuskure a' abinda yake ba na Addini ba. Amma duk da haka Allah ba zai musu hisabi akan kusakuren dasukai ba.