ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)*

Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu



⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪

*ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)* 

 *HADISI NA 9*

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " رُبَّ أَشْعَثَ مَدْفُوعٍ بِالْأَبْوَابِ، لَوْ أَقْسَمَ عَلَى اللَّهِ لَأَبَرَّهُ ".

FASSARA
An karɓo daga Abu Hurairah (R.A). Haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya kasance; gashinsa ya duddunƙule (saboda rashin wanka), jikinsa ya yi kaca-kaca (saboda tsabar talauci), wanda idan ya yi sallama za a tsayar da shi a bakin ƙofa (saboda tsabar talaucinsa): da zai yi rantsuwa ga Allah (kan wani abu), tabbas da sai Allah ya kuɓutar da shi!"
Muslim ne ya rawaito

DARASI
- Allah (S.W.T) ba ruwansa da dukiya ko kuɗi da ɗan adam ya mallaka, Allah ya fi ƙaunar zuciya mai taƙawa da ayyuka na ƙwarai.
- Duk wanda ya ke da taƙawa ga Allah (S.W.T) ko da a ce shi ya fi kowa talauci a garinsu, da zai roƙi Allah wani abu, tabbas sai Allah ya amsa masa, saboda kusancinsa ga Allah.
- Kada mu raina mutum musulmi don mun ganshi a cikin talauci da babu! Muminai su ne masu girmama dangogin mutane ba tare da kallon wani abu da suka mallaka na kuɗi ko mulki ba

Za mu ci gaba bayan awanni 24 in sha Allah

© Adam Sharada
12th Safar, 1442
20th September, 2021

Comments

Popular posts from this blog

Nana Khadija (R.A)

177 Sunan Tirmizi

Riyadus Salihin