ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)*

Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu


⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪

ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)

DARASI NA 2

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَجُلًا قَالَ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : أَوْصِنِي ؟ قَالَ : " لَا تَغْضَبْ ". فَرَدَّدَ مِرَارًا، قَالَ : " لَا تَغْضَبْ ".

FASSARA
An karɓo daga Abu Hurairah (R.A), haƙiƙa wani mutum ya ce da Annabi (S.A.W): Ka yi min wasiyya. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce masa "Kada ka yi fushi". Sai mutumin ya ƙara maimaita tambayar. Sai Annabi (S.A.W) ya sake ce masa "Kada ka yi fushi".

DARASI
Daga cikin kyawawan halaye ababen yabo ga Musulmi akwai haƙuri, wanda shi ne kishiryar fushi. Haƙuri sifface cikin kyawawan siffofin Manzon Allah (S.A.W). Fushi da hawan dokin zuciya suna sanya ɗan adam faɗawa cikin ɓarna. A cikin haƙuri (domin Allah) akwai lada da samun daraja.

Za mu ci gaba bayan awanni 24 in sha Allah.


*© Adam Sharada*
6th Safar, 1443
13th September, 2021

Comments

Popular posts from this blog

Nana Khadija (R.A)

177 Sunan Tirmizi

Riyadus Salihin