ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)
Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu
⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪
ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)
HADISI NA 3
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ : " أَعْذَرَ اللَّهُ إِلَى امْرِئٍ أَخَّرَ أَجَلَهُ حَتَّى بَلَّغَهُ سِتِّينَ سَنَةً ".
FASSARA
An karɓo daga Abu Hurairah (R.A), Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Allah ya gama ba da hanzari ga mutumin da aka jinkirta ajalinsa, har ya kai shekaru sittin (60)"
Bukhari ne ya rawaito
DARASI
Wannan hadisin yana koya mana; duk wanda Allah (S.W.T) ya bawa tsawon rayuwa a duniya, to an gama ba shi cikakkiyar dama wajen aikata ayyukan ɗa'a, da nisantar ayyukan saɓo. Kamar Annabi (S.A.W) yana faɗa mana mu yi amfani da lokacinmu da muke da jini a jika, mu kusancin Allah ya ayyukan alkhairi, gabanin girma ya cimmana.
Za mu ci gaba bayan awanni 24 in sha Allah.
© Adam Sharada
7th Safar, 1443
14th September, 2021
Comments
Post a Comment