ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)
Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu
⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪
*ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)*
*HADISI NA 4*
عَنْ أَبُو هُرَيْرَةَ ، عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَنَّ دَاوُدَ عَلَيْهِ السَّلَامُ كَانَ لَا يَأْكُلُ إِلَّا مِنْ عَمَلِ يَدِهِ.
FASSARA
An karɓo daga Abu Hurairah (R.A) daga Annabi (S.A.W) ya ce: "Haƙiƙa Annabi Dawud (A.S) ya kasance ba ya ci sai (daga) abin da hannunsa ya aikata."
ANNABI DAWUD (A.S)
- Allah (S.W.T) ya aiko shi da Manzanci kuma ya ba shi littafin Zabura (Suratun Nisa'i: 163).
-Allah (S.W.T) ya bawa Annabi Dawud (A.S) fasaha ta iya bayani (Suratu Sād: 20).
- Yana cikin Annabawan da Allah (S.W.T) ya aikowa Banu Isra'eela.
- Alƙur'ani ya ambaci suna Annabi Dawud sau 16 a cikin surori 9.
DARASI
- Hadisin yana koya mana ƙoƙarin neman na kai. Kada musulmi ya zama cima-zaune.
- Akwai yabo ga Annabawa da siffanta su da jarumta da ƙarfin zuciya. Ta yadda ba sa roƙo ko maula.
- Yana kuma koya mana muhimmancin neman halaliya. Da ciyar da kai daga halal, domin kuɓutar da gangar jiki da ruhi daga azabar Allah (S.W.T)
Za mu ci gaba bayan awanni 24 in sha Allah.
Telegram
© Adam Sharada
8th Safar, 1443
15th September, 2021

Comments
Post a Comment