Ana bude 'kofofin sama a kullum a dai dai lokacin Azahar domin masu addu'o'i da Neman biyan bukata!!!
Ana bude 'kofofin sama a kullum a dai dai lokacin Azahar domin masu addu'o'i da Neman biyan bukata!!!
_____________________
~ "Sallolin Nafila raka'o'i hudu kafin sallar Azahar suna bude wa mutum kofofin sama, wanda yayi wadannan salloli raka'o'i hudu kafin Azahar dai dai yake da wanda yayi salloli acikin dare a tsakiyar dare".
🎤:
Inji Manzon Allah (S.A.W).
Karanta "Sil-silah Sahiha" - Hadisi na 1,431.
Wasu mutane sun tambayi Manzon Allah me yasa yake yin raka'o'i hudu kafin sallar Azahar, sai Manzon Allah yace "Saboda a lokacin Allah yake bada umarni a bude kofofin sama, akan shigar da aiyukan alkhairin zuwa gare shi".
~ Karanta Sunanu Abu Dawud, hadisi na 3,128.
Nana Aisha (R.A) tace "Manzon Allah ya kasance yakan yi sallolin Nafila raka'o'i hudu bayan sallar Azahar idan bai samu damar yi ba kafin sallar Azahar din".
Karanta Sunanut Tirmiziy, hadisi na 426.
~ Wani mutum ya tambayi Manzon Allah yace:
"Raka'o'i hudu kafin sallar Azahar din nan ana yin tahiya ayi sallama a tsakanin su ne? sai manzon Allah yace a'a ba'a yi".
Abin nufi:
Zaka ka kawo raka'o'i hudu ne gaba dayan su, babu zaman tahiya a raka'o'i biyun farko, sai ka kammala sai kayi tahiya kayi sallama.
~ Jama'a ku dinga kiyaye wannan lokacin kuyi wadannan sallolin, ka roki Allah a wadannan lokacin kafin ayi Azahar, wallahi zaka ga abubuwan da zasu Kara maka Imani da kuma wadanda zasu baka mamaki.
~ Sheikh Muhammad Nasir yace:
"Wadannan sallolin ana yin su ne bayan an idda kiran sallah, kafin a shiga Azahar din".
~ Matukan kayi wadannan sallolin, ana so ka zauna a wurin ka dade kana addu'a, ka daga hannun ka sama, da ikon Allah idan ka lazimci wannan zaka samu mafita da sauki akan dukkan lamuran ka, da kuma matsalolin ka.
Domin manzon Allah yace ana bude kofofin sama, addu'o'in ka zasu samu karbuwa in sha Allah.
Lokaci ne mai tsananin tsadan gaske da yawan mu bamu bashi muhimmanci.
Allah yasa mu dace.
✍️
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.
Comments
Post a Comment