ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW)

Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu


Hadisi Na 06
⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " لَتُؤَدُّنَّ الْحُقُوقَ إِلَى أَهْلِهَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ، حَتَّى يُقَادَ لِلشَّاةِ الْجَلْحَاءِ مِنَ الشَّاةِ الْقَرْنَاءِ ". 

FASSARA An karɓo daga Abu Hurairah (R.A). Haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Lallai za a mayarwa da kowane mai haƙƙi haƙƙinsa ranar alƙiyama! Hatta akuya mai mara ƙaho, za a karɓar mata haƙƙinta daga akuya mai ƙago (idan ta taɓa tunkuyinta)." Muslim ne ya rawaito 

 DARASI - Yana bamu labarin adalcin Allah (S.W.T), wajen karɓarwa duk mai haƙƙinsa a hannun wanda ya zalunce shi a nan duniya. - Duk wani aiki da muke aikatawa a wannan duniya a rubuce yake, kuma tabbas sai Allah (S.W.T) ya yi mana hisabin ayyukanmu ranar alƙiyama. - Hadisin dalili ne akan tashin dabbobi da duk wata halitta mai rai a ranar alƙiyama. Domin yin hisabi tsakaninsu. - Idan har Allah (S.W.T) zai yiwa dabbobi hisabi, ya ƙwatowa mai haƙƙi haƙƙinta/sa tare da kasantuwar dabbobi ba su da hankali! Akwai tsoratarwa ga ɗan adam mai aikata zalunci da riƙe haƙƙoƙin mutane a hannunsa. 


 © Adam Sharada 10th Safar, 1443 18th September, 2021




Comments

Popular posts from this blog

Nana Khadija (R.A)

177 Sunan Tirmizi

Riyadus Salihin