ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)
Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu
⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪
ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)
HADISI NA 8
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " لَا يَسْتُرُ عَبْدٌ عَبْدًا فِي الدُّنْيَا، إِلَّا سَتَرَهُ اللَّهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ".
FASSARA
An karɓo daga Abu Hurairah (R.A). Daga Annabi (S.A.W) ya ce: "Babu wani bawa da zai suturta wani bawan a duniya, face (shi ma) Allah ya suturta shi ranar alƙiyama."
Muslim ne ya rawaito
FA'IDA
- Alƙur'ani ya ambaci kalmar الدنيا sau 115
- Alƙur'ani ya ambaci يوم القيامة sau 70
DARASI
- Yana koya mana taimakon juna da jin ƙai ga mabuƙata.
- Yana koya mana rufawa musulmi wanda ya faɗa cikin kuskure asiri, da kamewa daga yaɗa wani mummunan halinsa da ya ɓoyu.
- Yiwa mai aikata dangogin saɓo kamar shirka, bidi'a da manyan zunubai nasiha da nusarwa cikin hikima, yana cikin suturce musulmi daga masifa.
Za mu ci gaba bayan awanni 24 in sha Allah.
© Adam Sharada
11th Safar, 1443
19th September, 2021
Comments
Post a Comment