MUKULA DA WANNAN
MU KULA DA WANNAN 10 _Shin kun san `Abu Huraira`?_ Tambayar tawa za ta ba da mamaki, domin babu wani musulmi a doron ƙasa da bai san wanene Abu Huraira ba... Kwarai kuwa bana zaton akwai wanda ya taɓa shiga aji ko ya ziyarci karatukan malamai ba tare da ya san wannan bawan Allah. Abu Huraira asalin sunansa a Jahiliyya shi ne Abdush-Shams (Bawan Rana). Annabi Muhammad shi ne wanda ya sauya masa suna, a wata haɗuwa da sukai lokacin da Abu Hurairan ya gamu da Annabin rahama bayan ya karɓi musulunci. Sai masoyi S.A.W ya ke tambayar. Annabin Rahama: Yaya sunanka? Abu Huraira: Abdush-Shams Annabin Rahama: Sai dai Abdurrahman. Abu Huraira: Kwarai kuwa ya ma'aikin Allah, Mahaifina da Mahaifiyata fansa gareka. Wasu malaman kuma sun rawaici cewa sunansa Abdullahi. Yana da wata mage a lokacin yarintarsa, yana son wannan mage, sai sa'anninsa suke kiransa da Abu Huraira (Baban Mage). Saboda soyayya da mutuntawa kuwa Annabin Rahama yana kiransa da Abu Hirrin, kamar yadda yak...