MUKULA DA WANNAN
MU KULA DA WANNAN 10
_Shin kun san `Abu Huraira`?_
Tambayar tawa za ta ba da mamaki, domin babu wani musulmi a doron ƙasa da bai san wanene Abu Huraira ba... Kwarai kuwa bana zaton akwai wanda ya taɓa shiga aji ko ya ziyarci karatukan malamai ba tare da ya san wannan bawan Allah.
Abu Huraira asalin sunansa a Jahiliyya shi ne Abdush-Shams (Bawan Rana). Annabi Muhammad shi ne wanda ya sauya masa suna, a wata haɗuwa da sukai lokacin da Abu Hurairan ya gamu da Annabin rahama bayan ya karɓi musulunci. Sai masoyi S.A.W ya ke tambayar. Annabin Rahama: Yaya sunanka? Abu Huraira: Abdush-Shams Annabin Rahama: Sai dai Abdurrahman. Abu Huraira: Kwarai kuwa ya ma'aikin Allah, Mahaifina da Mahaifiyata fansa gareka. Wasu malaman kuma sun rawaici cewa sunansa Abdullahi. Yana da wata mage a lokacin yarintarsa, yana son wannan mage, sai sa'anninsa suke kiransa da Abu Huraira (Baban Mage). Saboda soyayya da mutuntawa kuwa Annabin Rahama yana kiransa da Abu Hirrin, kamar yadda yake taƙaita sunan wasu masoyansa daga cikin sahabbai kamar Nana Aisha da Sayyadina Usman Ibn Affan, daɗin daɗawa Hirrin din muzuru yake nufi, kuma abin sani shi ne muzuru yafi mage alheri. Abu Huraira kuwa ya kasance yafi son a kirashi da wannan suna da Annabin rahama ya kirashi da shi har ma yana cewa _Masoyina manzon Allah ne ya kirani d sunan._ Abu Huraira ya musulunta a hannun Ɗufail Bn Amru Addausiy, bayan ya musulunta kuma ya zauna cikin mutanensa har sai ana shekara ta shida bayan Hijira sannan suka zo tare da mutanen *Daus* sukai mubaya'a da nuna goyon bayansa ga Annabin rahama. A rayuwarsa tare da Annabin Rahama, ya tare a masallacin Annabi, kasancewar bai da iyali, ya lazimci Annabin rahama da hidimta masa, bai da kowa sai tsohuwar mahaifiyarsa, wadda a karon farko yayi iyakar ƙoƙarinsa akan ta musulunta amma ta ce ba ta san wannan zance ba. A ƙarshe ya je yana kuka yana yiwa Annabin Rahama magiya akan ya yiwa mahaifiyarsa Addu'a ta musulunta, ai kuwa Annabin Rahama yayi mata addu'ar shiriya... Take kuwa Abu Huraira yana tafiya gida sai gashi ya dawo yana kukan farin ciki yana yiwa Annabin Rahama bushara da musuluntar mahaifiyarsa. Ganin haka farin ciki ya cika zuciyar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, idanuwansa suna kallon irin farin ciki da nishaɗi da daya daga cikin masoyansa (Abu Huraira) yake. Ya kasance yana mutuƙar son Manzon Allah, har yana cewa `Ban taɓa ganin wani abu mai kyau, kuma mai haske ba, irin manzon Allah, kai kace rana ce take gudana a fuskarsa saboda haske.` Za mu taƙaita a nan. A rubutu na gaba za mu ji irin kwaɗayinsa wajen neman ilmi da kuma dagewarsa gami da soyayyarsa ga ilmin. Allah ya ƙarawa rayuwawarmu albarka, ya bamu ikon amfanuwa da ilmin da ya gangaro mana daga wajensu. Ameen. ✒️ Abu Umar Alkanawy
Comments
Post a Comment