Posts

H

1. #Annabawa Allah ta'ala yana zabar Annabawa da manzanni daga cikin mutane domin su shiryar da su sukuma yi kira izuwa gabautar Allah. Farkon Annabi shine Annabi Adam na karshe kuma cikamakin Annabawa shine Annabi Muhammad (s.a.w), bayansa babu wani Annabi da zaizo. Dukan su 'yan uwa juna, a i'mani sanan kuma masu kirane zuwa da a bautawa ubangijinsu. Dukk da dokokinsu sun banbanta amma suna yada aqeeda iri daya (itace bautawa Allah shi kadai) Dukan manzanni Allah ya tsare su daga kirkirar wani abu dazuwciyar su take so. Kamar yin hukunci da sarran su, fadawa manyan zunubai, ragi ko qari a addini. Basa aikata haka Allah yakaresu. Allah ya shiryar dasu da aikata nagarta a dukkan al amuransu na rayuwa. Duk dacewa su ma mutanene, zasu iya yin kuskure a' abinda yake ba na Addini ba. Amma duk da haka Allah ba zai musu hisabi akan kusakuren dasukai ba.

#Sabuwar Shekara1441.

Mun shiga Sabuwar Shekarar musulunci, Shekarar da ta wuce zataimana Shaida wanda yasamu kyakkyawar Shaida wanna shine ya rabauta. Wanda kuma yasamu akasin haka to yayi kokarin gyara kuskurensa. Hakika bulowar Rana da da wata da caccanzawar yanayi ayoyine ga ma'abota hankali Tafiyar kwanaki Alamace datake nuna muna cin wani yanki na rayuwar mu, tafiya mukeyi lokaci bai dawowa, nesantar Daniya Muke kusantar lahira muke. Muyiwa kanmu bincike inda mukai Aikata  kyakkyawan aiki sai mucigaba inda mukai kuskure mu gyara muduba muga mai mukatanadar a nan gaba . Mutuba daga zunuban mu mubar cewa sai nan gaba domin rayuwar mu ba a hanunn mu take ba. Muduba Abinda yai saura na rayuwar mu domin muyi aiki nagari, mu gaggauta aikata Alkairi.  mu Shiga Sabuwar Shekara da kyakkyawan fatan Samun nasara Da cigaba a dukkan Al'amuran mu na da kyautatawa Allah zato Zai kawo mana Sauqi Arayuwar mu Insha Allah. *1 Al-Muharram 1441* *1 September 2019* #IshaqShuaibuIbrahim