ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)*

Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu Telegram ⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪ *ZAƁAƁƁUN HADISAN ANNABI (S.A.W)* *HADISI NA 9* عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : " رُبَّ أَشْعَثَ مَدْفُوعٍ بِالْأَبْوَابِ، لَوْ أَقْسَمَ عَلَى اللَّهِ لَأَبَرَّهُ ". FASSARA An karɓo daga Abu Hurairah (R.A). Haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya kasance; gashinsa ya duddunƙule (saboda rashin wanka), jikinsa ya yi kaca-kaca (saboda tsabar talauci), wanda idan ya yi sallama za a tsayar da shi a bakin ƙofa (saboda tsabar talaucinsa): da zai yi rantsuwa ga Allah (kan wani abu), tabbas da sai Allah ya kuɓutar da shi!" Muslim ne ya rawaito DARASI - Allah (S.W.T) ba ruwansa da dukiya ko kuɗi da ɗan adam ya mallaka, Allah ya fi ƙaunar zuciya mai taƙawa da ayyuka na ƙwarai. - Duk wanda ya ke da taƙawa ga Allah (S.W.T) ko da a ce shi ya fi kowa talauci a garinsu, da zai roƙi Allah wani abu, tabbas sai Allah ya amsa masa, saboda ku...