Domin Kira Zuwa ga Addinin Musulunci da Raddi ga Miyagun Aƙidu ⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪⚪ ZAƁABƁUN HADISAN ANNABI (SAW) HADISI NA 3 عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ : " أَعْذَرَ اللَّهُ إِلَى امْرِئٍ أَخَّرَ أَجَلَهُ حَتَّى بَلَّغَهُ سِتِّينَ سَنَةً ". FASSARA An karɓo daga Abu Hurairah (R.A), Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Allah ya gama ba da hanzari ga mutumin da aka jinkirta ajalinsa, har ya kai shekaru sittin (60)" Bukhari ne ya rawaito DARASI Wannan hadisin yana koya mana; duk wanda Allah (S.W.T) ya bawa tsawon rayuwa a duniya, to an gama ba shi cikakkiyar dama wajen aikata ayyukan ɗa'a, da nisantar ayyukan saɓo. Kamar Annabi (S.A.W) yana faɗa mana mu yi amfani da lokacinmu da muke da jini a jika, mu kusancin Allah ya ayyukan alkhairi, gabanin girma ya cimmana. Za mu ci gaba bayan awanni 24 in sha Allah. © Adam Sharada 7th Safar, 1443 14th September, 2021